Isa ga babban shafi
Haba

Al’ummar Habasha na fama da Yunwa

Wata kungiyar jin kai na Save the Children ta ce sama da al’ummar Habasha miliyan 10 ne za su bukaci tallafin abinci a shekarar mai zuwa, sama da adadin mutane miliyan 8.2 dake cikin yunwa a bana a kasar, sakamakon mumunar fari da kasar ke cigaba da fuskanta.

Matsalar Fari a Habasha na Kamari
Matsalar Fari a Habasha na Kamari AFP PHOTO/GIANLUIGI GUERCIA
Talla

Karfin Tattalin arzikin Habasha shine dogaro da Noma, wanda kashi 1 cikin 3 na al’ummar kasar miliyan 90 ke rayuwa a kai.

Sai dai sauyin yanayi da rashin damuna na yiwa kasar babban illa, inda a yanzu mutane wannan kasar ke cikin matsanancin yunwa.

A wannan shekarar sama da mutane miliyan 8 ke bukatar taimako, kamar yadda gwamnati kasar da Majalisar dinkin duniya ke cewa, majalisar na kuma gargadi cewa akwai yiwuwar zuwa badi adadin ya ninka zuwa miliyan 15.

John Graham na kungiyar Save the Children ya ce, a hasashen su sama da al’ummar Habasha miliyan 10 ne za su fuskanci Karin abinci a badi.

Masana dai na cigaba da gargadi cewa da yiwuwar kasar Habasha ta tsinci kanta a fari mafi muni irinsa na farko cikin shekaru 50, muddin ba a dau matakan ceto al’ummar kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.