An bukaci bangarorin Libya su sasanta
Wakilan Manyan kasashen Duniya masu karfi da kuma wakilan kasashen Larabawa sun bukaci bangarorin da ke rikici a kasar Libya su rungumi tayin zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara don samar da Gwamnatin hadaka.
Wallafawa ranar:
Sakataren waje na kasar Amurka John Kerry na daga cikin Ministocin kasashe 20 da suka halarci taron da aka yi a Rome domin tattauna rikicin kasar Syria, inda aka gaza samun zaman lafiya tun bayan kawar da Shugaba Muammar Gaddafi a shekara ta 2011.
Kerry ya fadi cewa rikicin kasar Libya ya dauki lokaci sosai, kuma burin manyan kasashen duniya ne na ganin an sami zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Yace hakkin manyan kasashen duniya ne su ga lallai zaman lafiya ya dawo a Libya.
Wasu jami’an kasar Libya 15 da ke wakiltan sassa daban-daban suka shiga tattaunawar zaman lafiyan.
Wakilan kasar Libyan sun kushi wakilan majalisar kasar da ke da mazauni a Tripoli da kuma wakilan wata majalisar da ke da mazauni a Tobruk, kuma dukkan su sun amince su rattaba hannu cikin yarjejeniyar zaman lafiyan ranar Laraba a Morocco.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu