Paulina ta Rwanda za tayi zaman gidan yari shekaru 47
Hukumomin Rwanda sun sanar da sauya hukuncin daurin rai da rai da aka yiwa tsohuwar Ministar Matar kasar Pauline Nyiramasuhuko, wanda ke da hannu a kisan kare dangi Rwanda na shekara ta 1994.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka dai Pauline mai shekaru 69 za ta zauna a gidan yari har na tsawon shekaru 47, kuma a shekara ta 2011 aka same ta da laifin taka rawar gani a kisan kiyashin a yakin Butare da ke kudancin Rwanda, bayan ta kasance a tsare tun watan yulin shekara ta 1997.
Shi ma dai dan cikinta mai suna Arsene Shalom wanda ya jagoranci ‘yan tawaye a lokacin rikicin an yanke masa hukuncin zama gidan yari na tsawon shekaru 47.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu