Isa ga babban shafi
Najeriya-Kenya

Buhari zai fara ziyara Kenya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fara ziyarar kwanaki uku a kasar Kenya a yau Laraba domin halartar bikin karrama Sojojin kasar da mayakan Al Shebaab suka kashe a ranar 15 ga watan Janairu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari statehouse
Talla

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud na cikin shugabannin da zasu halarci bikin karrama Sojojin a Eldoret a Kenya.

Kungiyar al Shebab tace sojojin Kenya kimanin 100 ta kashe a harin da ta kai sansanin dakarun Afrika AMISOM a makon jiya.

Kakakin shugaban Najeriya Femi Adesina ya fadi a cikin wata sanarwa cewa shugaba Buhari zai kuma yi ganawa ta musamman da shugaba Uhuru Kenyatta kan huldar kasuwanci tsakanin Najeriya da Kenya.

Cikin wadanda zasu raka shugaban sun hada da Ministan harakokin waje da Ministan Kudi.

Sannan Shugaban zai wuce zuwa Habasha domin halartar taron shugabannin kasashen Afrika a birnin Addis Ababa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.