Isa ga babban shafi
Faransa

Ayrault zai karfafa diflomasiyar Faransa da sauren kasashe

Shugaban kasar Faransa Francois Hollade ya yiwa gwamnatin kasar garambawul kwana biyu da ficewar Laurent Fabius a mukaminsa na Ministan harakokin wajen kasar.Tsohon Firaministan kasar Jean Marc Ayrault ne aka damkawa nauyi tafiyar da ofishin ministan harakokin wajen kasar. 

Jean Marc Ayrault sabon Ministan harakokin wajen Faransa
Jean Marc Ayrault sabon Ministan harakokin wajen Faransa REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Denis Bauchard wani massani harakokin diflomasiyar Faransa ya sheidawa gidan rediyo faransa sashen faransanci cewa da sauren aiki musamman a kokarin sa na dinke barakar ficewar Laurent Fabius daga Gwamnatin Faransa, Francois Hollande Shugaban kasar ya sake dawowa da Jean Marc Ayrault tsohon Firaministan kasar a kujerar Ministan harakokin wajen Faransa.

Ficewar Laurent Fabius daga cikin Gwamnatin Faransa na a matsayi wata sheida dake nuna zahiri cewa farin jinin Shugaban kasar ya rage ainu ga idanu faransawa,
Fabius zai shugabantar hukumar fasaltar kudin tsarin mulkin Faransa.
Abin lura a nan shine cewa da dama daga cikin ma su lura da siyasar Faransa Francois hollande a wannan karo zai yi ikacin kokarin sa na gani ya sake faranta ran faransawa domin tunkarar zabubukan shekarar 2017 inda yanzu hakka ,alkaluma na nuni cewa Manuel Valls na fuskantar suka daga yan kasar kan wasu daga cikin matakan da ya dau zuwa kamfanonin kasar.

Wasu cibiyoyin bicinke a kasar sun futar da alkaluma dake nuna cewa mutane uku daga cikin faransawa hudu ma su zabe kwatankwocin kashi 75 cikin dari na masu zabe na nuna shaku game da sake zaben Francois Hollande a kujerar Shugabanci kasar a shekara ta 2017.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.