Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Compaore ya samu takardar zama dan kasar Cote d’Ivoire

Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore ya karbi takardar shaidar zama dan kasar Cote D’Ivoire, inda ya ke gudun hijira tun bayan korar sa daga karagar mulki a watan Oktoban 2014.

Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara tare da tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaore
Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara tare da tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaore presidence.ci
Talla

Kafofin yada labaran Cote d’Ivoire sun ruwaito cewa tun a watan Janairu ne tsohon shugaban ya samu takardar zama dan kasa tare da kaninsa, amma sai a jiya gwamnatin kasar ta sanar.

Rahotanni sun ce shugaba Alassane Ouattara ne ya sanya hannu kan umurnin ba tsohon shugaban takardar sheda zama dan kasar Cote d’I voire tun a watan Nuwamba bayan shugaban ya gudo zuwa cikin kasar.

A watan Disemba Burkina Faso ta bada sammacin kamo shugaban kan tuhumar da taka rawa wajen kisan tsohon shugaban kasar Thomas Sankara.

Dr Ali Sakola Jika, malami a jami’ar Ouagadougou ya ce sakamakon bayar da wannan takardar shaidar zama dan kasa, zai kasance abu mai wuya a taso keyar Compaore zuwa Burkina Faso domin fuskantar shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.