Isa ga babban shafi
Burundi

Kungiyar Tarayyar Africa za ta aika da wakilai 200 zuwa Burundi

Kungiyar Tarayyar Africa na shirin tura wakilai 100 na kungiyar kare hakkin bil’adama da wasu Dakaru 100 da za su kunshi sojoji don ganin irin wainar da ake toyawa a kasar Burundi.

Shugaban Africa ta kudu  Jacob Zuma tare da mai masaukinsa  Pierre Nkurunziza
Shugaban Africa ta kudu Jacob Zuma tare da mai masaukinsa Pierre Nkurunziza STRINGER / AFP
Talla

Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma ya sanar da haka yayin wata ziyara da ya jagoranci kaiwa Bujumbura.

Shugaba Jacob Zuma har ya tattauna da Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza.

Cikin ayarin Jacob Zuma akwai shugabannin kasashen Senegal da Gabon, da kuma na Mauritania, da Fira Ministan Habasha inda suka duba yadda za'a kawo karshen rikicin Burundi na tsawon watanni goma.

Kungiyar Tarayyar Africa za ta samar da masu sa idanu daga kungiyar kare hakkin bil’adama su 100 da kuma soja guda 100 da za su sa idanu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.