Isa ga babban shafi
Kamaru

Wakilin RFI Ahmed Abba zai gurfana gaban Kotun soji a kamaru

A yau litinin, Ahmed Abba, wakilin Sashen Hausa na rfi zai bayyana karo na farko a gaban kotun soji da ke birnin Yaounde a kasar Kamaru, bayan share tsawon watanni ana tsare da shi a asirce.

Wakilin Sashen hausa rfi a Kamru Ahmed Abba
Wakilin Sashen hausa rfi a Kamru Ahmed Abba
Talla

An dai kama Ahmed Abba a ranar 30 ga watan Yulin 2015 a garin Maroua da ke arewacin kasar, kafin daga bisani a kai shi wani wuri inda ake tsare da shi a asirce.

Gurfanar da shi a gaban kotu wani muhimmin ci gaba ne a kokarin da RFI ke yi na ganin cewa an bai wa lauyansa Barrister Tchoungang damar sanin dalilan da suka sa hukumomi ke tsare da shi.

Tuni dai Hukumar gudanarwa ta RFI ta fassara illahirin rahotanni da hirarrakin da Abba ya rika turowa a matsayin sa na wakilin rediyon a Kamaru, kuma wadannan bayanai ne da za su bayar da dama domin kare shi a gaban kotu tare da tabbatar da cewa ya gudanar da aikinsa a cikin ka'ida.

Gidan Radio France International rfi, har ya zuwa yau na kallon wakilinsa Ahmed Abba a matsayin wanda ba shi da laifi, kuma yana fatan bangaren shari'a na kasar Kamuru zai yi masa adalci ta hanyar tabbatar da gaskiya a wannan shari'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.