Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Zuma ya tsallake rijiya da baya

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya a kuri’ar yankan kaunar da aka kada a Majalisar dokokin kasar a yau Talata sakamakon adawar da shugaban ke fuskanta ga tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Shugaban kasar Africa ta Kudu, Jacob Zuma.
Shugaban kasar Africa ta Kudu, Jacob Zuma. REUTERS/Nic Bothma/Pool/Files
Talla

Zuma ya samu nasara a Majalisar bayan samun kuri’u 222 akan 99 daga bangaren ‘Yan Jam’iyyarsa na ANC.

A karo na biyu ke nan a shekara guda, Majalisar dokokin Afrika ta Kudu ta kada kuri’ar yankan kauna domin yunkurin tsige shugaba Jacob Zuma sakamakon zarginsa da aikata laifin cin hanci da rashawa.

Tun bayan da ya sallami ministocin kudin kasar guda biyu a tsakanin ‘yan kwanaki a watan Disamban bara, Shugaba Jacob Zuma ya shiga tsaka mai wuya.

Jam’iyyar ‘yan adawa ta Democratic Alliance ce ta bukaci a gudanar da kur’ar yankan kaunar akan Zuma yayin da jagoran jamiyyar, Mmusi Maimane ke cewa, al’ummar Afrika ta kudu na son a dora laifin tarbarbarewar tattalin arzikin kasar akan Zuma.

Wata sanawar da ta fitar, Jam’iyyar ta ce, kada kuri’ar yankan kaunar ita ce hanya mafi dacewa da za ta bayar da damar tsige shugaba Zuma daga kan mukaminsa.

Amma jam’iyyarsa ta African National Congress ke da rinjaye a majalisar, inda ta ke da kashi 62 cikin 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.