Isa ga babban shafi
Nijar

An soma Kamfen a Zaben Nijar zagaye na biyu

A yau Talata aka kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da za a gudanar zagaye na biyu a Jamhuriyyar Nijar a ranar 20 ga watan Maris tsakanin Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou da abokin hammayarsa Hama Amadou da ake tsare da shi.

Hama Amadou da Mahamadou Issoufou.
Hama Amadou da Mahamadou Issoufou. AFP/Issouf Sanogo/Farouk Batiche/Montage RFI
Talla

Wannan na zuwa ne bayan kotun kundin tsarin mulki ta amince a je zagaye na biyu bayan amincewa da sakamakon zaben farko da aka gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairu.

 Zaben ya shiga zagaye na biyu ne bayan Shugaba Mahamadou Issoufou na PNDS Tarayya ya samu kashi 48.43 na kuri’u yayin da kuma Hama Amadou na Moden/Lumana ya zo a matsayi na biyu da kashi 17.73.

 Tsohon Firaminista Seini Oumarou shi ne ya zo a matsayi na uku da yawan kuri’u kashi 12.12, sai tsohon Shugaban kasa Mahamane Ousmane da ya zo a matsayi na hudu da kashi 6.25. Amadou Boubakar Cisse daya daga cikin manyan ‘Yan adawa ne ya zo a matsayi na biyar.

Tuni bangaren ‘Yan adawa da suka amince su marawa Hama Amadou baya a zagaye na biyu wanda ake tsare da shi kan badakalar mallakar ‘ya’ya da aka yo fataucinsu daga Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.