Isa ga babban shafi
Faransa-Congo

Faransa ta bayyana damuwarta kan zaben Congo

Faransa ta bayyana damuwar ta kan yadda hukumomin kasar Congo suka katse wayoyin sadarwa da intanet lokacin da aka gudanar da zaben shugaban kasar inda ta bukaci tabbatar da gaskiya a zaben.

Shugabam kasar Congo Denis Sassou-Nguesso
Shugabam kasar Congo Denis Sassou-Nguesso PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Romain Nadal ya ce an gudanar da zaben shugaban kasar cikin yanayi mara kyau.

Nadal ya ce Faransa na bin diddigin yadda zaben ya gudana da kuma neman ganin an baiwa al’ummar kasar abinda suka zaba.

Sai dai a cewar Gwamnatin Congo, ta dau matakan katse layukar sadarwa da Intanet ne saboda tsaro.

Sakamakon farkon zaben Congo ya bayyana a cewa Shugaban kasar  Denis Sassou Nguesso shine ke kan gaba wurin lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.