Isa ga babban shafi
Congo

'Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Congo

Sakamakon wucen gadi na zaben Congo Brazzaville, ya nuna cewa shugaban kasar mai ci Denis Sassou Ngesso na dab da lashe zaben, abinda zai ba shi damar tsawaita zamansa akan karagar mulki yayin da 'yan adawa su ka yi watsi da sakamakon tare da fadin cewa za su fitar da nasu a yau Laraba.

Shugaban Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso
Shugaban Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Shugaban hukumar zaben kasar, Henri Bouka ya shaida wa manema labarai cewa, Sassou Nguesso wanda ya jagoranci kasar fiye da shekaru 30, ya samu kashi 67 cikin 100 a sakamakon da aka tattara a yankuna 72 daga cikin yankuna 111.

To sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban kawancen kungiyar ‘yan adawa, Charles Bawao ya yi watsi da sakamaon, inda ya ce ba shi da inganci kuma ya saba da abinda suka sani a zahiri.

‘Yan adawar dai na shirin fitar da nasu sakamakon a yau, abinda gwamantin kasar ta ce karan tsaye ne ga doka.

Rahotanni sun ce, gwamnatin kasar ta tsawaita wa’adin katse hanyoyin sadawar ne saboda gudun yada sakamakon karya da ya saba da na hukumomi, abinda ta ke ganin zai iya haifar da rikici.

A bangare guda, a yayin da 'yan adawa ke bayyana shakku game da sakamakon, jami’an tsaro kuwa sun dukufa ne wajen aikin sintiri a titinan babban birnin kasar ta  Congo Brazzaville.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.