An saki Hama Amadou jagoran adawa a Nijar
Kotun daukaka kara a Nijar ta bayar da belin Hama Amadou jagoran adawa da aka garzaya da shi asibitinin Faransa daga gidan kaso kan tuhumarsa da fataucin ‘yaya daga Najeriya, wannan na zuwa ne bayan kammala zaben shugaban kasa da Issoufou Mahamadou ya lashe.
Wallafawa ranar:
Kotun ta bayar da umurnin sakin Hama a yau Talata, kamar yadda Lauyan da ke kare shi Mossa Boubakar ya tabbatar.
Tun a ranar 16 ga watan Maris ne aka garzaya da Hama zuwa Asibitin Faransa daga gidan kaso a yayin da ya rage kwanaki a gudanar da zabe zagaye na biyu tsakanin shi da Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou.
‘Yan adawa sun kauracewa zaben saboda rashin sakin Hama, tare da yin watsi da sakamakon zaben da Issoufou ya lashe da sama da kashi 92.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu