Isa ga babban shafi
Somalia

Mutane 3 sun mutu a harin bam a Somalia

 Bam da aka dasa a cikin mota daf da gidan sayar da abinci a yau asabar, ya fashe tare da hallaka mutane 3 da kuma jikata wasu biyar a tsakiyar kasar ta Somaliya, an tabbatar da cewa dukkan mutanen da al’amarin ya shafa fararen hula ne.

Wani harin da ake zargin kungiyar EL-Shabab da kaiwa a Somalia
Wani harin da ake zargin kungiyar EL-Shabab da kaiwa a Somalia AFP/Abdurashid Abdulle
Talla

Kakakin karamar hukumar yankin birnin Mogadishu Abdifatah Oumar ne ya shedawa manema labarai yadda al’amarin ya auku da kuma yawan mutanen da suka rasa rayukansu.

Sai dai Oumar yace zai yi wuya a san ko su waye suka kai wannan harin a yanzu duk da cewa hare-hare irin wannan baya rasa nasaba da ayyukan kungiyar Alqaida ko El-shabab dake ci gaba da tayar da kayar baya a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.