Isa ga babban shafi
Ethiopia

'Yan bindiga sun kashe mutane 208 a Habasha

Hukumomin kasar Habasha sun ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da wasu 'yan bindigan Sudan ta kudu suka kai kasar ya kai 208, yayin da aka sace yara kanana 108.

'Yan bindigan Sudan ta kudu sun kashe mutane 208 a Habasha
'Yan bindigan Sudan ta kudu sun kashe mutane 208 a Habasha bussinessinsider.com
Talla

An dai kai harin ne a  ranar juma’ar da ta gabata a yankin Gambela wanda ya ke dauke da ‘yan gudun hijira dubu 284 da suka gudu daga Sudan ta kudu saboda kaucewa tashin hankalin da ake fama da shi a kasar.

Getachew Reda, wani jami’i a yankin ya ce, adadin ya tashi jiya zuwa mutane 208 daga 140 da aka kidaya a ranar Asabar.

Bayan sace yara guda 108, an kuma sace dabbobin da suka kai 2,000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.