Isa ga babban shafi
UNHCR-MIGRANTS

UNHCR: Bakin haure 500 ake furgaban sun mutu a teku

Hukumar 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ta ce bakin haure akalla 500 ne ake kyautata zaton sun mutu sanadiyar hadarin da kwale-kwalen da suke ciki ya yi a tekun Mediterranean.

Bakin haure a kan Teku
Bakin haure a kan Teku REUTERS/Marina Militare
Talla

A cewar Carlotta Sami, mai Magana da yawun hukumar, wasu daga cikin bakin 41 da aka ceto daga tekun ne suka bayar da labarin hadarin da kuma alkalluman yawan mutanen da suka soma wannan balaguron tare.

Yawancin bakin hauren ‘yan asalin kasashen Somalia da Sudan da kuma Habasha ne, sai kuma wasu kalilan da suka fito daga kasar Libya.

Rayukan daruruwan bakin haure ne ke salwanta kusan kullum a tekun mediterrranean, yawanci wadanda ke tserewa yake-yake a kasashensu zuwa Nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.