Isa ga babban shafi
Turai

Ministocin Turai na taro kan matsalar bakin haure

A yau juma’a ne ministocin ‘yankin Turai ke gudanar da taro domin tattauna matsalar bakin haure da ke ci gaba da kwarara kasashensu mafi yawansu daga Syria da kuma Iraqi.

Matsalar bakin haure na ci gaba da ta'azzara a kasashen Turai.
Matsalar bakin haure na ci gaba da ta'azzara a kasashen Turai. REUTERS/Marko Djurica
Talla

To sai dai kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi gargadi a game da yiyuwar daukar matakin tasa keyar bakin daga wasu kasashen Turai zuwa Turkiyya.

Jean-Francois Dubost, daya ne daga cikin jami’ai a kungiyar ta Amnesty ya kuma ce, abin da suke nema shi ne a fayyace karara kasashen da aka tabbatar da cewa idan an mayar da ‘yan ci rani, to za a kare lafiyarsu.

Mr. Dubost ya kara da cewa, Idan aka yi la’akari da ka’idojojin karbar baki na kasashen Turai, za a tarar cewa kasar Turkiya ba za ta iya cika wadannan ka’idoji ba, kuma a wannan yanayi zai kasance abu mai hatsari a tasa keyar bakin hauren da suka shiga Turai zuwa kasar Turkiya.

"Kowa ya tabbatar da cewa Turkiya na tursasa wa bakin haure, akwai wani lokaci ma da jami’an tsaron kasar suka rika bude wuta da bindiga a kan su, saboda haka ya zama wajibi a lura da wannan lamari na kare lafiyar ‘yan ci rani" inji Mr. Dubost.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.