Isa ga babban shafi
Afrika

Kasashen tafkin Chadi za su kara kaimi a yaki da ta'addanci

Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi sun bayyana cewar duk da nasarorin da aka samu wajen yaki da kungiyar Boko Haram, ya zama wajibi kasashen su ci gaba da jajircewa domin ganin bayan kungiyar baki daya.

Shugaban Faransa Francois Hollande da takwaransa na Najeriya  a taron tattauna matsalar Boko Haram
Shugaban Faransa Francois Hollande da takwaransa na Najeriya a taron tattauna matsalar Boko Haram REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Taron shugabannin yankin wanda ya samu halartar shugaban Faransa Francois Hollande, da wakilan kasashen Birtaniya da Amurka da aka gudanar a Abuja, ya bayyana cewar dole duniya ta hada kai wajen goyan bayan yakin da kuma sake gina yankin.

Duk da dai Birtaniya ta yaba da irin rawar da Najeriya da makwabtanta ke takawa wajen kakkabe mayakan na Boko Haram, amma ta ce har yanzu yakin bai kare ba kamar yadda  Philips Hammond, sakataren harkokin wajen Birtaniya  ya bayyana a taron.

Mr. Hammond ya ce, rundunar soji ta taka rawar gani mai kayatarwa amma har yanzu ba a kakkabe mayakan ba.

A cewar Hammond ya zama dole a kalubalanci akidar Boko Haram mai guba matukar dai ana bukatar kawar da kungiyar baki daya.
 

Shi kuwa mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken wanda ya wakilci John Kerry a taron na Abuja kan matsalar Boko Haram, ya yi kira ne ga dakarun tsaro da su gudanar da aikinsu ta hanyar mutunta hakkin dan adam, inda ya ce, take hakkin fararen hula, na  tinzira su har su dauki tsattsaurar akida, abinda ke kara rura wutar matsalar ta'addanci.

Mr. Bliken ya ce, sun yaba wa Najeriya da Nijar da Chadi da Kamru da Benin kan yadda suka kafa rundunar hadaka domin yaki da Boko Haram.

Ga dai cikakken rahoton da Abdurrahman Gambo Ahmad ya hada mana

01:26

Kasashen tafkin Chadi za su kara kaimi a yaki da ta'ddanci

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.