Isa ga babban shafi
Najeriya

Kamaru za ta dawo da ‘Yan gudun Hijirar Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta cim ma yarjejeniya da gwamnatin Kamaru da kuma Majalisar Dinkin Duniya kan maido da ‘yan gudun hijirar Boko Haram dubu 80 da ke zaune a Kamaru.

Dubban 'Yan gudun Hijira ne suka tsallaka Kamaru saboda rikcin Boko Haram
Dubban 'Yan gudun Hijira ne suka tsallaka Kamaru saboda rikcin Boko Haram AFP/Issouf Sanogo
Talla

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ce ta sanar da haka bayan samun jituwa tsakanin Najeriya da Kamaru.

Kakakin hukumar agajin gaggawa NEMA a Najeriya Sani Datti, ya ce za dawo da ‘Yan Najeriya ne da suke son su dawo kasarsu.

A can baya dai Kamaru ta taso keyar wasu dubban ‘Yan Najeriya ba da son ransu ba, akan haka ne kuma kasashen biyu suka cim ma yarjejeniyar dawo da wadanda ke ra’ayin dawo wa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.