Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Rudani ya hana kare masu hijira a Sudan ta Kudu

Majalisar dinkin duniya ta ce, tababa kan shugabanci da kuma dokokin duniya kan aikin sojojin samar da zaman lafiya suka haifar da matsala wajen kai dauki a lokacin da aka kai kazamin hari kan sansanin 'yan gudun hijirar da majalisar ta ajiye fararen hula kusan 50,000 a Malakal da ke Sudan ta kudu.

Lokacin da aka kai harin a sansanin na Malakal da ke Sudan ta Kudu
Lokacin da aka kai harin a sansanin na Malakal da ke Sudan ta Kudu Justin LYNCH / AFP
Talla

Mai magana da yawun majalisar dinkin duniya, Stephane Dujjaric ya ce binciken da hukumar majalisar ta gudanar ya nuna cewar, akwai rudani kan shugabancin sojojin da ke aikin samar da zaman lafiya a lokacin da aka kai harin, abinda ya haifar da matsalar aikin kare 'yan gudun hijirar.

Majalisar ta ce tana nazari kan shawarwarin da aka ba ta da suka kunshi rawar da sojoji da 'yan sandan da aka dorawa alhakin kare 'yan gudun hijirar suka taka da kuma kasashen da suka fito.

Kungiyoyin agaji irin su Medicins Sans Frontier sun zargi dakarun da ke aikin samar da zaman lafiyar da kasa kai dauki sansanin 'yan gudun hijirar da aka kai harin har sai bayan sa’oi 16, lokacin da aka kashe fararen hula 30 aka kuma raunana 123 a tashin hankalin da aka kwashe kwanaki biyu ana yi a Malakal.

Wani bincike na daban, ya nuna cewar kokarin shigar da makamai sansanin 'yan gudun hijirar da wasu sojoji suka yi, shi ya haifar da tashin hankalin tsakanin kabilun Shiluk da Nuer da kuma Dinka da Dafuri.

Yau ake saran shugaban aikin samar da zaman lafiya Harve Ladsous ya yi wa kwamitin sulhu bayani kan rahotan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.