Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

Da hannun gwamnati a kashe yara a Sudan ta Kudu inji MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce gwamnatin Sudan ta Kudu ce ta taimaka wajen hallaka al’ummar kasar sakamakon damar da ta baiwa sojinta na yiwa mata fyade da kuma kona kananan yara da ransu, abinda Majalisar tace laifi ne babba da ya keta hakin bil’adama

Yara a yankin Darfur da yaki ya raba da gidajensu
Yara a yankin Darfur da yaki ya raba da gidajensu
Talla

Rahotan Majalisar Dinkin Duniya na cewa yawanci daga cikin daruruwan mutanen da suka rasa rayukansu a yakin basasar Sudan ta Kudu na daga cikin wadanda sojojin gwamnati suka kashe da gangan

Rahotan ya kuma bayyana yadda gwamnatin Sudan ta kudu ke kaiwa sojojin mata a maimakon biyansu hakkinsu inda aka samu mayakan da laifin yiwa matan fyade, akwai kuma lokuta da dama da sojojin ke kona yara kanana da ransu abinda tuni Majalisar Dinkin Duniya ta Kwatanta da rashin imani tsantsa da ya kuma keta hakkin bil’adam.

Sabon binciken wannan kazamin kisa da kuma fyaden ya yi karo da sakamakon rahoton kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty a baya dake zargin gwamnatin Sudan ta kudu da laifin hannu a hallaka wasu mutane 60 cikin su da yara kanana da aka kulle a motar dakon kaya har sai da suka mutu.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gudanar da binciken cikin gaggawa don hukunta wadanda keda hannu a ciki wannan danyen aikin

Shekaru 2 da ballewar Sudan ta kudu daga kasar Sudan kasar ta fada cikin yakin basasa al’amarin da ya kai ga rasa rayukan mutane fiye da 500,000 da kuma tilastawa sama da miliyan 2 tserewa daga muhallinsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.