Isa ga babban shafi
Liberia- US

Matar Shugaban Amurka Ta bukaci Mata a Liberiya da su Nemi Ilmi

Uwargidan Shugaban kasar Amurka Barack Obama, Michelle Obama ta roki ‘yan mata a kasar Liberia da su nemi ilmi kuma su nace da son zuwa makaranta ko ta wani hali.  

Uwargidan Shugaban Amurka Michelle Obama
Uwargidan Shugaban Amurka Michelle Obama REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Michelle Obama na Magana ne yau a yayinda ta ke ziyara a kasar Liberia.

A watan biyar na bara Uwargida Michelle Obama ta kaddamar da wani shiri a kauyen Kakata don yekuwa ga iyaye su goyi bayan ilmin mata.

Uwargidan Obama wadda lauya ce da ta sami ilmi daga shahararriyar Jami'ar Havard ta ce ilmi ne yasa ta sami suna da daukaka da take dashi yanzu haka.

‘Ya‘yan ta biyu Malia mai shekaru 17 tare da Shasha mai shekaru 15 suka rufa mata baya yayin wannan ziyara a kasar Liberia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.