Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta kudu

An ji karar harbe-harbe a birnin Juba

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa, an ji karar harbe-harben bindiga a babba birnin Juba a yammacin jiya Alhamis, yayin da jami’an soji suka dakile wasu hanyoyin wucewa da ke yankin Gudele. 

Shugaban Sudan ta Kudu Salva  Kiir da mataimakinsa Riek Machar
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar Reuters/Stringer
Talla

Wani mazaunin birnin na Juba, mai suna Ramadan Kazimiro ya ce, ya ji karar harbe- harben bindiga a wurare da dama na birnin.

Shi kuwa wani mutun da ya bukaci a sakaya sunansa cewa ya yi, an yi harbe harben ne a yankin Gudele da ke kusa da yammacin Juba, inda mataimakin shugaban kasar Riek Machar ke da gida.

Jami’an soji sun yi amfani da motocinsu wajen dakile tsakiyar hanyar da ta ratso daga Gudele, abinda ya hana shige da ficen jama’a da ke yankin.

Shaidun gani da ido sun ce, jama’a na cikin halin fargaba a Juba inda wasun su ke ta guje-guje domin shiga gidajensu saboda tsoron cewa, wata babbar tarzoma za ta sake kunno kai har ta ritsa da su.

Tun a watan Disamban shekara ta 2013 ne jinjirar kasar Sudan ta Kudu, ta tsindima cikin tashin hankali bayan shugaba Salva Kiir ya kori mataimakinsa Riek Machar.

Kasar dai na fama da matsalar tattalin arziki tun lokacin da ta samu nakasu wajen samar da man fetir sakamakon rikicin da ta gamu da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.