Isa ga babban shafi
Zamfara

‘Yan Majalisar Zamfara sun lissafa laifuka 11 na tsige Yari

Majalisar Jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta bayyana dalilan da suka sa ta ke kokarin tsige Gwamnan Jihar Abdulaziz Yari Abubakar Mafara.

Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara
Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara wordpress.com
Talla

Wata sanarwa da ‘Yan Majalisun suka fitar bayan wani zama a Kaduna, sun lissafa laifuka 11 da suke zargin Gwamnan da aikatawa wadanda suka ce ya sabawa doka.

Laifufukan da ‘Yan Majalisun suka lissafa sun hada da karkata akalar naira biliyan 11 tallafin da aka karbo daga Gwamnatin Tarayya, da kuma naira biliyan guda na tallafin noma da aka karbo daga Babban Bankin Najeriya.

‘Yan Majalisun sun kuma sanya kin mayar da kudaden fansho da gratuti ga hukumomin da suka dace gwamnan ya yi, da kuma takaddamar nada shugaban kula da ilimin bai-daya a mataki na farko Murtala Adamu Jangebe da Majalisa ta ki amincewa saboda batan kudi naira biliyan guda na hukumar.

Sai kuma zargin gwamnan da zama shanshani wanda ba ya zama jihar don gudanar da ayyukan da suka rataya akansa.

Sannan ‘Yan Majalisar sun zargi Gwamnan da bayar da umurnin kama shugabanin Majalisar sakamakon yunkurin tsige shi.

Sanarwar da ‘Yan Majalisar suka fitar sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga tsakaninsu da gwamnan da ke amfani da jami’an farin kaya a matsayin barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.