Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Fyade a Yankunan hakar Ma'adanai ya tsananta inji MSF

Wani Bincike a kasar Afirka ta kudu ya nuna cewar kowacce mace daya daga cikin mata 4 dake Yankin da ake hakar ma’adinin Platinum ta fuskanci fyade a rayuwar ta inji kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontier.

Mace daya daga cikin mata 4 dake Yankin da ake hakar ma’adinin na fuskanci fyade a Afrika ta Kudu
Mace daya daga cikin mata 4 dake Yankin da ake hakar ma’adinin na fuskanci fyade a Afrika ta Kudu mage by: Gallo Images/Thinkstock
Talla

Kungiyar agajin ta Medicins Sans Frontier tace ta gudanar da bincike kan mata 800 masu shekaru tsakanin 18 zuwa 49 a Yankin Rustenberg dake Arewa maso Gabashin Johannesburg a cikin watanni biyu bara, kuma binciken ya tabbatar da cewar cikin ko wadanne mata 4 an yiwa guda fyade.

Garret Barnwell, jami’in jinkai na kungiyar yace abin taikacin shine idan akayi la’akari da kididigar da akayi za a iske cewar an yiwa mata kusan 11,000 fyade kowacce shekara.

Rahotan ya ruwaito wata jami’ar kula da lafiyar dake cewar, fyade ya zama jiki ga akasarin matan dake rayuwa a wanan Yankin, kuma kashi 5 ne kacal ke zuwa asibiti dan samun kula saboda kunya.

A kasar Afirka ta kudu mutane sama da miliyan 6 ne ke fama da cutar sida, wanda shine kashi 11 na al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.