Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta fara rigakafin Polio a Borno

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da gagarumin shirin rigakafin cutar Polio a Yankin Arewa Maso Gabashin kasar sakamakon samun yara biyu da cutar.

Rigakafin cutar Polio
Rigakafin cutar Polio AFP PHOTO / GWENN DUBOURTHOUMIEU
Talla

Minstan lafiya Isaac Adewole ya ce jami’ansu sun fara aikin don ganin an dakile yaduwar cutar wadda a baya aka shirya wanke kasar daga cikin kasashen da ke fama da ita.

Ana sa ran aikin rigakafin ya samu goyan bayan kasashen Chadi da Kamaru wadanda ke makwabtaka da Yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Najeriya dai ta yi bikin cika shekaru biyu ba tare da an samu wanda ya kamu da cutar Polio ba a kasar, a wani mataki da aka yi hasashen nahiyar Afrika na dab da bankwana da cutar baki daya.

Cutar dai ta fi shafar yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar, wacce ke haifar da nakasar jiki ko mutuwa.

A baya can dai, Najeriya ta kasance cikin kasashen da ke sahun gaba inda cutar ta fi kamari, amma yanzu kasashen Afghanistan da Pakistan ne akan gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.