Isa ga babban shafi
Burundi

Manyan jami'an tsaro na tserewa

Rahotanni sun ce a kalla manyan jami’an Rundunonin Soji da ‘Yan sandan kasar 13 ne suka tsere daga kasar a farkon watan Agusta.

Masu gudun hijira daga kasar Burundi
Masu gudun hijira daga kasar Burundi Reuters
Talla

Wani mai sharhi kan al’amuran tsaro a kasar Burundi Gratien Rukindikiza ya ce manyan jami’an tsaron sun arce daga kasar ne saboda tsoron kada masu adawa da gwamnatin kasar su kai musu hari, saboda goyon bayansu ga gwamnati mai ci, ko kuma kasancewarsu 'yan kabilar Hutu.

Sai dai kuma kakakin rundunar sojin Burundi ya musanta cewa manyan jami’an tsaron sun tsere ne saboda fargabar rashin tsaro da batun kabilanci, kasancewar yawancin jami’an gwamnatin kasar ‘yan kabilar Hutu ne yayin da kuma a garkame ‘yan Tutsi masu yawa a kurkuku.

Tun a watan Yulin daya gaba ne a shekara ta 2015 rikicin siyasa ya yi kamari a Burundi sakamakon nasarar da Shugaba Pierre Nkurunziza yayi na lashe zaben kasar, rikicin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.