Isa ga babban shafi
Burundi

Majalisar dinkin Duniya ta koka bisa cigaba da rikici a Burundi

Majalisar dinkin duniya ta bukaci kasar Burundi, ta gaggauta daukar matakan dakile keta hakkin bil adama, kisan daruruwan fararan hula da kabilanci dake dada yawaita a kasar.

Masu zanga zanga a Burundi
Masu zanga zanga a Burundi STR / AFP
Talla

A cewar Majalisar tana da rahotanni dake nuna yadda ake amfani da manufar siyasa wajen aikata kisa, tare da rura wutar rikicin kabilanci.

Burundi ta fada cikin rudanin siyasa bayan da Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta zarcewa a shugabancin kasar, har yanzu an gaggara shawo kan rikicin dake cigaba da mamaye kasar.

Rikicin siyasar yayi sanadin raba dubunnan mutane a kasar rasa gidajensu, da yawa daga ciki kuma na gudun hijira a makwabtan kasashe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.