Isa ga babban shafi
Burundi

Ana zanga-zangar adawa da tura ‘Yan Sanda 1,000 a Burundi

Sabuwar zanga-zanga ta barke a Burundi domin adawa da matakin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince na tura ‘Yan sanda kimanin 1,000 a kasar mai fama da rikici.

Burundi na zanga-zangar adawa da matakin tura 'Yan sandan wanzar da zaman lafiya a kasar
Burundi na zanga-zangar adawa da matakin tura 'Yan sandan wanzar da zaman lafiya a kasar STR / AFP
Talla

Rahotanni sun ce hukumomin Burundi ne suka shirya zanga-zangar domin adawa da matakain na Majalisar Dinkin Duniya.

Masu zanga-zangar sun hada gangamin ne Bujumbura a daidai ofishin jekadancin Faransa wacce ta gabatar da bukatar tura ‘Yan sanda dubu a kasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar suna rike da sakwannin da ke sukar Faransa akan ita ke bukatar jami’an wanzar da zaman lafiya saboda hare haren da ta ke fuskanta.

Tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ayyana matakin neman wa’adin shugabanci na uku Burundi ta fada cikin rikici.

Daruruwan ‘Yan kasar ne suka tsallaka zuwa Rwanda domin fargabar ballewar yakin basasa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.