Burundi
Jami'an AU na aikin sa ido a Burundi
Kungiyar kasashen Afirka ta ce, yanzu haka kashi daya bisa uku na jami’anta 200 da aka amince ke aikin sa ido a kasar Burundi.
Wallafawa ranar:
Talla
Su dai jami’an da suka hada da sojoji da kuma masu kare hakkin Bil Adama za su sa ido ne kan abinda ke faruwa a kasar sakamakon zargin cin zarafin jama’a da ake yi wa jami'an gwamnati.
Rahotanni sun ce rashin kai jami’an 200 ya biyo bayan matsayin gwamnatin kasar na cewar, sai ta tantace daukacin wadanda za a kai kafin su shiga kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu