Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

Salva Kiir ya amince da karin dakarun wanzar da zaman lafiya.

Shugaba Kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya amince da rarrashin gwamnatinsa da kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na ganin ya amince da shirin tura Karin dakarun samar da zaman lafiya 4.000 dan magance tashe tashen hankulan da ake samu a kasar.

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da sakataren MDD Ban-Ki-moon à birnin Juba.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da sakataren MDD Ban-Ki-moon à birnin Juba. REUTERS/Jok Solomon
Talla

Tawagar wakilan da ya ziyarci Juba babban birnin kasar a karshen mako ya jaddada muhimmancin kai dakarun dan kare lafiyar fararen hula da kuma dubban mutanen da rikicin ya raba da gidajen su.

A baya jama’a da ke gudun hijira a kasar sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta gaggauta tura Karin dakarun saboda mawuyacin halin da suka sami kansu.

Gwamnatin Sudan ta Kudu dai ta ki amincewa da Karin dakarun wanzar da zaman lafiyar 4000, inda ta ke bayyana hakan a matsayin wani yanayi na yunkurin mamaye kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.