Isa ga babban shafi
Gabon

Bongo ya zargi EU da nuna son kai a zaben Gabon

Shugaban Gabon Ali Bongo ya zargi masu sa ido na kungiyar tarayyar Turai da nuna son kai bayan da suka bayyana cewa an tabka kura-kurai a zaben shugabancin kasar da aka ayyana Bongo a matsayin wanda ya yi nasara.

Shugaban Gabon, Ali Bongo
Shugaban Gabon, Ali Bongo AFP
Talla

Bongo mai shekaru 57 ya zargi masu sa idon da nuna goyon baya ga abokin hamayyarsa Jean Ping kuma ya ce, kotun kolin kasar ce kawai za ta iya bayar da umarnin sake kidaya kuri’u.

Tun bayan sanar da sakamakon zaben ne a watan jiya, kasar ta Gabon mai arzikin man fetir ta tsindima cikin tashin hankali, abinda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

A jiya ne, tawagar ta masu sa ido daga Turai ta ce, zaben ya gamu da kura-kurai a lardin Haut-Ogooue, tushen shugaba Bongo, inda ya lashe kashi 95 cikin 100 na kuri’un da aka kada a yankin.

Sai dai Bongo ya mayar da martani ga tawagar, inda ya ce, ai ya kamata a duba abinda ya faru a yankin da abokin hamayyarsa Jean Ping ke da karfin fada-a-ji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.