''Akwai damuwa kan yadda Sudan ta kudu ke takurawa fararen hula''
Dakarun Samar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu sun bayyana damuwar su kan yadda gwamnatin kasar ke tirsasawa kungiyoyin fararen hular da suka yi Magana da wakilan kwamitin sulhu da suka ziyarci kasar makon jiya.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce jami’an tsaron gwamnati na yiwa kungiyoyi fararen hular barazana saboda bayanan da suka bai wa jami’an Majalisar Dinkin Duniya.
Wakilan Majalisar sun je Juba dan janyo hankalin gwamnatin kasar na amincewa da kai Karin sojojin samar da zaman lafiya.
Har yanzu ana ci gaba da gani yadda za a dawo da kwanciyar hankali na din-dindin a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu