Isa ga babban shafi
EU-AFRIKA

EU za ta tallafawa Afrika don dakile Bakin haure

Kungiyar Tarrayar Turai ta shirya kaddamar da asusun tallafawa al’ummar kasashen Nahiyar Afrika da ke jefa rayuwarsu cikin hadari a kokarin tsallaka teku don zuwa Turai don inganta rayuwarsu.

Bakin haure na ci gaba da kwarara Turai duk da matakan da ake dauka
Bakin haure na ci gaba da kwarara Turai duk da matakan da ake dauka 路透社/Antonio Parrinello
Talla

Wannan dai na a matsayin alkawarin da shugaban hukumar Tarrayar Turai Jean Claude Juncker ya yi a baya inda ya ce kungiyar za ta tunkari matsalar baki ‘yan ciranin da ke kwarara cikin nahiyar Turai.

Kungiyar dai ta bukaci taimakon kasashen na EU don ganin sun bayar da gudunmawa don tara akalla Euro Biliyan arba’in da hudu kudin da Juncker ya ce zai taimakawa tattallin arzikin kasashen nahiyar Afrika, inganta arzikin nahiyar zai kuma samarwa matasa aikin yi.

Juncker ya bayyana damuwarsa kan asarar rayukan dubban ‘yan cin rani da ake samu kusan ko wane mako a kokarinsu na tsallaka teku a kananan kwale- kwale.

Akalla baki ‘yan cirani sama da miliyan daya ne suka tserewa yaki da yunwa daga kasashensu zuwa nahiyar turai a bara.

Shugaban ya kara yin kira zuwa ga masu hannu da shuni dama ‘yan kasuwa wajen bayar da tallafi tare da kokarin saka hannayen jari a Nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.