Isa ga babban shafi
Morocco

Jam’iyyar Musulmi ta lashe zaben Morocco

Jam’iyyar ‘yan uwa musulmi ta Justice and Development Party (PJD) mai mulki a Morroco ta lashe zaben Majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Juma’a. Jam’iyyar ta Firaminista Abdelilah ta lashe kujeru 125 cikin 395, yayin da mai adawa da ita ‘Yamiyyar (PAM) ta lashe kujeru 102.

Abdelilah Benkirane, jagoran Jam'iyyar PJD a Morocco
Abdelilah Benkirane, jagoran Jam'iyyar PJD a Morocco REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Tun a 2011 jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta PJD ke mulki a Morocco bayan zanga-zangar da ta kawo karshen karfin ikon Sarki Muhammad na biyar a kasar.

Jam’iyyar Istiglal ce ta zo a matsayi na uku wacce ta yi gwagwarmayar samun ‘Yancin kai daga Turawan Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.