Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya barke a garin Malakal a karshen mako kamar yadda majiyar soji ta sanar.

Garin Malaka da ke Sudan ta Kudu
Garin Malaka da ke Sudan ta Kudu Justin LYNCH / AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan tawaye sun yi barazanar karbe garin, yayin da kuma suka kai farmaki kan gidajen gwamnati a ranar jumma’ar da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Lul Ruai Koang ya bayyana cewa, sojoji sun yi nasarar fatattakar ‘yan tawayen tare da kashe 56 daga cikinsu

Koang ya kara da cewa, maharan ba su samu nasarar karbe iko da garin Malaka ba kamar yadda suka yi buri a baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.