Isa ga babban shafi
Kenya

An yi gasar Kyau ta Zabaya a Kenya

A karon farko a Afrika an gudanar da gasar kyau tsakanin Zabaya a kasar Kenya inda aka zabi Sarki da Saruniyar Kyau a Nairobi babban birnin kasar.

Zabaya na fuskantar wariya a Afrika
Zabaya na fuskantar wariya a Afrika AFP
Talla

A sassa da dama na Afrika Zabaya na fuskantar wariya da kalubale na farautar sassan jikinsu domin wasu tsafe tsafe, amma a Kenya sun ware dare guda domin nuna baiwar da Allah ya yi masu.

A ranar Juma’a aka gudanar da bikin na Zabaya wanda wani Zabaya dan majalisar dokoki Isaac Mwaura ya shirya.

Dan Majalisar ya ce ya shirya bikin ne domin yakar wariya da suke fuskanta tare da tabbatar wa duniya cewa za a iya samun zabaya masu kyau.

Isaac Mwaura ya ce rashin samun ilimi da ayyukan yi, na daga cikin abubuwan da ke ci masu tuwo a kwarya.

A wasu kasashen gabashi da kudancin Afrika da suka hada da Tanzania da Malawi da Burundi da Mozambique ana sace Zabaya ana kashe su don yin tsafi da wasu sassan jikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.