An tarwatsa masu zanga-zanga a Guinea Bissau
Daruruwan mutane ne suka shiga zanga zanga a kasar Guinea Bissau don ganin an sake gudanar da zaben shugabancin kasar, yayin da kungiyar ECOWAS ke kokarin ganin an aiwatar da wata yarjejeniyar shekara guda da za ta magance rikicin siyasar kasar.
Wallafawa ranar:
Masu zanga zangar dauke da alluna daban-daban da ke dauke da rubuce rubuce, sun yi tattaki zuwa fadar shugaban kasar da ke Bissau kafin 'yan sanda su tarwatsa su.
Kasar Guinea Bissau ta yi ta fama da juyin mulki har sau 9 tun shekarar 1980, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa, rashin magance rikicin kasar na iya bai wa masu safarar kwayoyi damar karbe mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu