Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan fashi sun addabi kauyukan Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara arewacin Najeriya sun ce ‘Yan bindiga sun kai kai hare hare a wasu kauyukan kananan hukumomin Maradun da Shinkafi da Maru inda suka kashe mutane da dama tare da sace wasu.

Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali
Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali NTA
Talla

Majiyoyi daga yankin Maradun sun ce kusan mutane 30 aka kashe a harin da ‘Yan bindigar suka kai a kauyen Dan Kamoji a jiya Juma’a.

Sannan wasu ‘Yan bindigar da dama sun shiga kauyen Tubali saman Babura a gundumar Birnin Yero cikin karamar hukumar Shinkafi inda suka suka kashe mutane da dama.

A yankin Maru ma rahotanni sun ce maharan sun sace mutane sama da 40 ‘Yan kasuwa da ke hanyar zuwa cin kasuwar Magami tare da kashe ‘Yan sanda biyu a kauyen Ningyado da ke cikin yankin Dansadau.

Sai dai rundunar ‘Yan sandan Jihar ta ce tana bincike domin tantance adadin mutanen da aka kashe a jerin hare haren.

Kakakin ‘Yan sandan Jihar Muhammad Shehu ya shaidawa RFI Hausa cewa har yanzu ba su tantance adadin mutanen da aka kashe ba.

Hare haren na zuwa bayan harin da aka kai wa lebarorin hako zinari a makon jiya a kauyen Bindin cikin karamar hukumar Maru inda aka kashe mutane kusan 40

‘Yan fashi dai sun addabi mutanen kauyukan Zamfara duk da farmakin da rundunar sojin Najeirya ta kaddamar na Operation Harbin Kunama a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.