Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta kara tsunduma cikin matsalar tattalin arziki

Alkalumman da hukumar Kiddidiga a Najeriya ta fitar na cewa tattalin arzikin kasar ya sake samun koma baya a cikin watanni uku da suka gabata sakamakon hare-hare da ake kai wa kan bututun mai a yankin Neja Delta da kuma karanci kudaden waje a hannun ‘yan kasuwa.

Takardar kudin Naira a Najeriya
Takardar kudin Naira a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Hukumar ta ce tattalin arzikin ya kara samun koma baya ne da sama da kashi 2.

Najeriya dai ta fada cikin matsalar tattalin arziki ne sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya inda farashin ya yi mugunyar faduwa daga dala 100 zuwa kasa da 50.

Hare haren da kuma tsagerun Neja Delta ke kai wa ya kara dada haifar da matsalar tattalin arzikin kasar da ke dogaro da arzikin mai.

Gwamnatin shugaba Buhari dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.