Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Robert Mugabe ya gargadi masu neman kujerar sa

Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe yayi kakkausar suka kan ya’an Jam’iyyar sa ta ZANU-PF dake kokowar mulki, inda ya gargade su da su kaucewa haka.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Yayin da yake jawabi ga taron Jam’iyyar a Harare, Mugabe yace Jam’iyyar na ta cikin shiri tareda bin mataki zuwa mataki na raba mukaman ta, saboda haka bai dace ace wasu daga cikin ya’an ta na gwagwarmayar samun mukamai ba.

Shugaba Mugabe da ya hau karagar mulki tun shekarar 1980 yaki bayyana ranar saukar sa bayan ya kwashe shekaru 92 a duniya, inda manyan jami’an sa ke ta fafatawa dan ganin sun gaji kujerar shugabancin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.