Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Sojan Zimbabwe Sun Ce Babu Ruwansu Da Batun Wanda Zai Maye Gulbin Mugabe

Rundunar sojan kasar Zimbabwe ta ce babu ruwan ta da batun wanda zai maye gulbin Shugaba Robert Mugabe, yayinda mutan kasar ke wasiwasin wanda zai maye gulbin Shugaban.

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe
Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe Reuters/Philimon Bulawayo
Talla

Robert Mugabe mai shekaru 92 ya kasance bisa madafun ikon kasar tun bayan samun ‘yanci aki daga Turawa cikin shekara ta 1980.

Sai dai yanzu haka ana ganin bashi da koshin lafiya sosai, al’amarin dake sa wasu ke tunanin waye zai iya maye gulbin sa idan ta Allah ta kasance.

Wasu kafofin labarai a cikin kasar na ganin watakila mataimakin shugaban Emmerson Mnangagwa ya iya rike kasar, amma kuma akwai wasu dake ganin matar Mugabe Uwargida Grace Mugabe ta iya rike mulkin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.