Isa ga babban shafi
Tunisia

Dubban 'yan Tunisia na adawa da dawowar mayakan sa kai

Sama da ‘yan kasar Tunisia 1,500 ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ginin majalisar dokokin kasar, don nuna rashin amincewarsu, bisa dawowar ‘yan asalin kasar da suka kasance mayaka a kungiyoyin ta’addanci.

Masu zanga zanga a birnin Tunis
Masu zanga zanga a birnin Tunis
Talla

Masu zanga zangar bayyana bacin ransu a kan jam’iyyar Ennahda, wadda ke da ra’ayin a yiwa ‘yan kasar da suka shiga karkashin haramtattun kungiyoyi afuwa tare da sake karbarsu, idan har sun tuba.

Zanga zangar na gudana dai dai lokacin da jami’an tsaro a kasar ta Tunisia suka sanar da kame mutane 3 wadanda ke da alaka da wani dan kasar Anis Amri da ya kai hari a kasuwar saida kayayakin Kirsimeti a birnin Berlin na Jamus.

Zalika a ranar Juma’ar da ta gabata, Ministan cikin gida na Tunisia, Hedi Majdoub ya shaidawa zauren majalisar kasar cewa, akalla ‘yan asalin kasar da suka fafata a matsayin sojin sa kai karkashin kungiyoyin ‘yan ta’adda ne suka dawo gida.

Wani rahoto da majalisar dinkin Duniya ta fitar ya ce akalla ‘yan asalin kasar Tunisia sama da 5,000 ne ke fafata yaki a matsayin sojin sa kai, karkashin haramtattun kungiyoyi musamman, wadanda ke kasashen Syria Iraqi da kuma Libya.

Tun bayan juyin juya hali a kasar da ya gudana a shekara ta 2011, Tunisia ta sha fama da hare haren kungiyoyin ta’addanci da yayi sanadin mutuwar jami’an tsaronta da suka kunshi sojoji da ‘yan sanda akalla 100, fararen hula 20 da kuma masu yawon shakatawa a kasar, ‘yan kasashen ketare 59.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.