Isa ga babban shafi
Duniya

Ta'addanci da Annoba sun hana yawon bude ido

Wani bincike ya nuna cewar hare haren ta’addanci, samun annoba da kuma matsalar bakin haure sun taimaka wajen rage adadin masu yawon bude ido da ke tururuwa kasashen musulmai.

Ta'addanci da annoba sun taimaka wajen rage yawan masu yawon bude ido a kasashen musulmai.
Ta'addanci da annoba sun taimaka wajen rage yawan masu yawon bude ido a kasashen musulmai. Reuters
Talla

Rahotan ya nuna cewar kasar Tunisia da ta yi fice wajen samun baki masu yawon bude ido, ta yi asarar baki sama da miliyan biyu a bara sakamakon harin da aka kai kasar, matsalar da ta shafi masu otel otel da wuraren cin abinci da kuma masu sayar da kayan al’adun kasar.

Hare haren bama-baman da aka samu a Turkiya ya sa kashi 40 cikin 100 na bakin da ke zuwa kasar sun kaurace mata.

Ita ma kasar Masar ta rasa dubban bakin da ke zuwa shakatawa a Sharm el Sheikh, matsalar da ta shafi tattalin arzikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.