Isa ga babban shafi
Burundi

An kashe Ministan muhalli a Burundi

Wasu ‘yan bindiga sun kashe ministan kare muhalli na Burundi Emmanuel Niyonkuru a birnin Bujumbura. Wanda wannan ne karon farko da aka kashe wani babban jami’in gwamnati bayan kasar ta fada cikin rudanin siyasa.

Mutane sun taru a inda aka harbe a Nyakabiga kusa da Bujumbura babban birnin Burundi
Mutane sun taru a inda aka harbe a Nyakabiga kusa da Bujumbura babban birnin Burundi AFP Photo/Carl de Souza
Talla

Kakakin ma’aikatar ‘yan sanda Pierre Nkurikiye, ya ce an harbe ministan ne a hanyarsa ta zuwa gida bayan kammala bukin shiga sabuwar shekara.

Kisan na zuwa bayan shugaban kasar Pierre Nkunrunziza ya sanar da aniyar sake gyara kundin tsarin mulki domin bas hi damar neman wa’adi na hudu a 2020, duk an samu lafawar rikici bayan ya zarce a wa’adi na uku.

Rundunar ‘Yan sandan kasar ta sanar da cafke wata mata da ake zargi tana da hannu a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.