Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta kafa dokar sa ido kan kungiyoyi masu zaman kansu

Majalisar kasar Burundi ta amince da kafa dokar da zata tsaurara kan sa ido bisa yadda kungiyoyi mazu zaman kansu na kasashen ketare zasu rika gudanar da ayyukansu a kasar. 

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ????
Talla

‘Yan majalisa 105 biyar ne suka goyi bayan dokar, a kuri’ar da suka kada, yayinda guda daya yaki goyon bayan matakin.

A karkashin dokar tilas ne baki dayan kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen ketare dake kasar, su rika ajiye kudaden tafiyar da ayyukansu na kasashen ketare, a asusunsu da ke babban bankin kasar, sannan kuma tilas su rika bawa gwamnati rahoton yadda suke tafiyar da harkokinsu a kasar ta Burundi duk bayan watanni 6, idan ba haka a kuma su fuskanci tsattsauran hukunci, koma da takisu ga ficewa daga kasar.

Kafa dokar na zuwa, bayanda shugaban kasar Pierre Nkurunziza, ya zargi ire-iren kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa, da ke kasar da goyon bayan boren da ‘yan adawa kasar ke yiwa gwamnatinsa.

Tun a watan yulin shekara ta 2015, Nkurunziza ya gabatarwa da majalisar kasar kudurin dokar, bayan sake lashe zaben shugabancin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.