Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta yanke alaka da Majalisar Dinkin Duniya

Gwamnatin Burundi, ta sanar da yanke hulda da hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar dinkin duniya, sakamakon rahoton da hukumar ta wallafa da ke zargin gwamnatin kasar da cin zarfin al'ummarta.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ????
Talla

Burundi ta dauki matakin ne, kwana guda bayan ta haramtawa jami’an hukumar 3, masu bincike tsoma baki cikin harkokin kasar, inda suka yi gargadin cewa kasar na iya komawa cikin yakin basasa.

A watan Disamba aka nada Pablo de Greiff na Colombia da Christof Heyns daga Afrika ta Kudu, sai kuma Maya Sahli Fadel na Algeria jagorancin bincika keta hakkin biladama a kasar Burundi.

Kuma rahotansu ya bayyana cewa gwamnatin kasar tana da hannu dumu dumu wajen cin zarafin mutane, kama daga azabtar da sama da mutane 1000 a kasar sai kuma fyade da jami’an kasar ke aikatawa

Ko a makon daya gabata, sai da Burundi ta sanar da shirinta na ficewa daga ICC, bayan da kotun hukunta manyan laifukan ta Duniya ta ce zata bincika rikicin siyasar da kasar take fama da shi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.