Manyan Jami'an Soja da na 'Yan Sanda na tserewa daga Burundi
A kasar Burundi, manyan sojoji da ‘yan sanda akalla 10 ne suka tsere suka bar kasar cikin wannan wata gudun kada a muzguna masu karkashin Gwamnatin Shugaba Pierre Nkurunziza.
Wallafawa ranar:
Wani masanin harkokin tsaron kasar Gratien Rukindikiza ya ce wadan da suka gudu sun zarce 13, kuma sun tsere ne sun bar kasar don fargaban abinda zai biyo baya saboda kabilar da suka fito ko kuma saboda ana zargin suna goyon bayan ‘yan adawa.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na zargin Gwamnatin Shugaba Pierre Nkurunziza wanda ‘yan kabilar sa ta Hutu suka fi yawa a ciki, da muzgunawa sauran kabilu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu