Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta amince ta fice daga kotun ICC

‘Yan majalisar dokokin Burundi sun amince kasar ta janye daga kotun duniya,  in da a yanzu ake sauraron majalisar dattawan don jin nata matsayin.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ????
Talla

‘Yan majalisa 94 ne suka amince da wannan mataki daga cikin 110, a wani mataki na nuna rashin amincewa da yunkurin da kotun ta duniya ke yi na binciken laifufukan kisa da cin zarafin bil’adama da ake zargin gwamantin Pierre Nkurunziza da aikatawa.

A farkon wannan shekarar ne, kotun ICC ta fara gudanar da bincike kan laifukan da ake da suka hada da azabtar da jama’a da kargame wasu a gidan yari har ma da yi wa mata fyade.

Burundi dai ta nuna bacin ranta bayan kotun ta ayyana sunayen manyan jami’an gwamnatin kasar da ake zargi da hannu a azabtar da ‘yan adawa da kuma kashe su.

A cikin watan Aprilun da ya gabata ne, kotun ta ICC ta bayyana cewa, rikicin siyasar Burundi ya yi sanadiyar mutuwar mutane 450 tare da tilasta wa dubban jama’a kaurace wa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.