Isa ga babban shafi
Gambia

ECOWAS ta soke ziyara a Gambia

Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika sun soke kai ziyara a wannan Laraba a kasar Gambia a kokarin shawon kan Yahya Jammeh don ganin ya mika ragamar mulki ga  Adama Barrow, in da aka dage kai ziyarar har zuwa ranar juma’a mai zuwa.

Shugaban Gambian Yahya Jammeh da shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya da Ellen Johnson Sirlef na Liberia da John Mahama na Ghana
Shugaban Gambian Yahya Jammeh da shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya da Ellen Johnson Sirlef na Liberia da John Mahama na Ghana Nigeria president Twitter account
Talla

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, duk da cewa an dage ganawar da aka tsara yi a yau laraba, amma fa matsayin shugabannin kasashen yankin na ganin cewa Jammeh ya mika ragamar mulki a karshen wa’adinsa na nan daram.

Wannan kuma na zuwa ne a wani lokaci da babban mai sharia na kasar Emmanuel Fagbenla ya sanar cewa, a cikin watan biyar ko na sha-daya za su saurari batun makudi da Yahya Jammeh ya ce an yi a zaben.

A farko dai shugaba Jammeh da ya mulki Gambia na tsawon shekaru 22 ya amince da shan kayi a zaben na watan jiya, amma daga bisani ya tubure bayan ya zargi jami'an hukumar zaben kasar da tafka kura-kurai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.